2 Yuli 2021 - 18:16
Ravanchi : Dole Ne Amurka Ta Ba Da Tabbacin Ba Za Ta Sake Ficewa Daga Yarjejeniyar Nukliya Ba

Jakadan Iran a Majalisar Dinkin Duniya ya ce dole ne Amurka ta bada tabbacin cewa ba za ta taba janyewa daga yarjejeniyar nukiliya Iran ba, wanda hakan yana da matukar muhimmanci ga makomar tattaunawar da ke gudana a Vienna da nufin farfado da yarjejeniyar ta 2015.

ABNA24 : Da yake magana da manema labarai bayan taron wamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a ranar Laraba, Majid Takht-Ravanchi ya sake nanata cewa ficewar Amurka daga yarjejeniyar nukiliyar, ya saba wa dokokin kasa da kasa.

"Amurka ta fice daga yarjejeniyar, ba tare da wani dalili ba," in ji shi.

Ficewar da Amurka ta yi daga yarjejeniyar a cikin shekarar 2018, a lokacin tsohon Shugaba Donald Trump, tare da laftawa Iran jerin takunkumi da kuma matsin lamba" shi ne ya sanya mahukntan Tehran maida martani ta hanyar jingine aiki da wasu sharudda da yarjejeniyar ta kunsa.

Tun daga watan Afrilu, ne wakilai daga Iran da ragowar kasashen da suka sanya hannu a yarjejeniyar ta 2015 – da suka hada da Faransa, Birtaniyya, Jamus, Rasha da China ke tattaunawa a Vienna da nufin dawo da Amurka a cikin yarjejeniyar.

342/